(ABNA24.com) A jawabinsa a zaman taron masana harkokin siyasa ta hanyar na’urar sadarwa da kungiyar Harkar Musulunci ta kasar Jodan ta shirya domin tunawa da cikan shekaru 53 mamaye birnin Qudus: Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Isma’il Haniyyah ya yi kira ga kungiyar Fatah mai jagorancin hukumar cin gashin kan Palasdinawa da ta hada kai da sauran kungiyoyin Palasdinawa domin daukan matakin bai daya kan batun Palasdinu.
Haniyyah ya kara da cewa: Manufar daukan matsayi na bai daya a tsakanin dukkanin kungiyoyin Palasdinawa ita ce samun shirye-shirye da tsare-tsare na bai daya da al’ummar Palasdinu ta amince da su domin cimma manufofinta.
Kamar yadda Isma’il Haniyyah ya yi kira kan samar da wani tsari na hadin gwiwa tsakanin Palasdinawa da al’ummar Jodan, kari kan haka, samar da wata hadaka da ta hada Larabawa da Musulmi yankin da nufin karfafa gwagwarmayar Palasdinawa a fagen neman hakkokinsu da za su kai ga samar da kasar Palasdinu mai cikakkiyar ‘yancin kai.
/129
8 Haziran 2020 - 06:07
News ID: 1044427
Kungiyar Hamas Ta Bukaci Hadin Kan Palasdinawa Domin Daukan Matakan Bai Daya